Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Bikin kaddamar da radar samfurin Hormuz ya gudana a yau Asabar, a karkashin jagorancin Kwamandan Rundunar Sojojin Sama ta Iran Birgediya Janar Ali Reza Sabahi Fard, da wasu mataimakansa.
Manufar aiwatar da aikin dai shi ne kara karfafa ayyukan kere-kere a bangaren makamai na kariya wadanda Iran din take samarwa, wanda wannan na’ura tana daga cikin sabbin ayyuka na samar da makaman da na’urori na zamani da bangaren kera makamai a ma’aikatar tsaro na kasar Iran ya gudanar.
Baya ga haka kuma an fitar da wasu sabbin nau’oin makamai masu linzamiua karon farko daga cikin makaman da kasar ta kera domin kariyar kai.
Kwamandan Rundunar Sojojin Sama ta Iran Birgediya Janar Ali Reza Sabahi Fard ya ce, gudanar da wannan gwaji yana daga cikin abubuwan da Iran take yi a halin yanzu domin kara zama cikin shirin ko ta kwana, domin fuskantar kowace irin barazana daga wajen kasar.
342/